Über Tun Fil'azal
Babu abin da zai faru da zai ba wa Allah mamaki. Tun fil'azal Ya shirya Ya halicce abu mai rai a duniya. Tun fil'azal Ya halicce mutane a cikin siffar Shi. Tun fil'azal Ya so Ya yi zumunci da kowannen mu. Kuma tun fil'azal Ya na da Shirin fansan mu.
"A sa'ad da Allah ya fara halittar Sama da duniya." - Farawa 1:1
Menene ya faru a lokacin da Allah Ya ke halittar duniya da dukkan abin da ke ciki? Menene ma'anar an halice mu a cikin siffar Allah? Menene ya faru a gonar a lokacin da Adamu da Hauwawu sun yi zunubi? Menene ya sa Allah Ya ba wa Adamu da Hauwawu zarafin samun 'ya'yan da aka hana su täawa? Ko da gaske ne ambaliyan ya mamaye duniya duk? Menene ya sa akwai bayyanen zuriya da dama a cikin Farawa? Menene ya faru a hasumiyan Babila?
Tun Fil'azal wani binciken Littafi mai Tsarki na tsawon mako shida akana Farawa 1 - 11. Wannan binciken zai bincika labarin halita, tushen mutum, sakamakon zunubi kan duniya, alkawali nan take na fansa, dalilin ambaliyan, tanadin Allah ga Nuhu da iyalin shi, yarjejeniyan Allah ta farko da mutum, da kuma zuriyan Mai Ceto.
Kodayake yin bincike da zurfi cikin Maganan Allah ya na kara kawo tambayoyin fiye da amsoshi, Tun Fil'azal zai tafi da kai tsaye cikin tunanin tauhidi da tambayoyin da mu ke fuskanta a cikin bangaskiyan mu. Yayin da mu ke binciken hanyan da Allah Ya halice mutum kuma Ya na zumuci da shi a farko, za mu koyi abubuwa da dama game da yadda Yak e aiki a cikin rayuwan mu da kuma a duniya a yau.
Ki häa kai da mu a yanan gizo domin wannan bincike na tsawon mako shida ko akan app namu na Love God Greatly. A can za ki samu abubuwan da ya shafi Tun Fil'azal a duka wurare biyu tare da rubuce rubucen mu na Litinin, Laraba da Jumma'a, da Karin bayyani ta wurin karat una kullum da kuma jamma'a masu kauna domin su karfafa ki yayinda ki ke biciken labaran halite a cikin Farawa 1-11.
Mehr anzeigen